7 Nuwamba 2021 - 11:41
​Malaman Addini Na Najeriya Da Masar Suna Tattaunawa Kan Wuce Gona Da Irin Daliban Addini

Wata tawagar malaman addini daga Jami’ar Al-Azhar ta kasar Masar ta na ziyarar kwanaki 5 a tarayyar Najeriya, inda tawagar tuni ta fara tattaunawa da malaman kasar don gano hanyoyin da za’a bullowa masu wuce gona da iri daga cikin daliban addini.

Kamfanin dillancin labaran NAN na tarayyar najeriya ya nakalto Dr Nazeer Ayad babban sakatarin cibiyar binciketna jami’ar Al-Azhar ya na cewa tawagar har’iala ta na dauke shirin daukar nauyin dalibai ‘yan Najeriya don karatu a mashahuriyar jami’ar ta Al-Azhar dake birnin Alkahira na kasar Masar.

Dr Ayad ya kara da cewa addinan Ibrahimiyya su na da abubuwa na asali da suka hadasu, ta yadda duk wanda ya fahinci addinin musulunci ba zai dauki ra’ayin wuce gona da iri da kuma kiyayya ga mabiyan sauran addinan Ibrahimiyya ba, wato kiristanci da kuma yahudanci ba.

342/